Kamar yadda sanarwa ta fito daga ofishi Firaministan Birtaninyar cewa, David Kemron da shugaban Masar Abdelfattah El’sissi sun tattauna ta waya gabanin ziyarar da zai kai birnin London.
Sun yarda da tsaurara matakan tsaron a filin jirgin saman da ke wajen shakatawar a Misira. Har yanzu dai ba wasu dalilan da aka bayyana na sanadiyyar hatsarin jirgin da ya hallaka mutane 224.
Wata na’urar tauraron dana dam din sojojin Amurka ta kyallaro hasken faduwar jirgin da ya fada yankin na Sinai.
Hukumomi dai suna kyautata zato an harbi jirgin da makami mai linzami ne kafin ya tarwatse ya fada nesa da tazarar kilomita 9,400 a saharar Sinai. Tuni dai jami’ar Masar suka shiga binciken musabbain faduwar jirgin.
Shugaban Masar ya yi watsi da jita-jitar cewa ‘yan kungiyar ISIS ne suka harbor jirgin kamar yadda ake yadawa.