Yana nufin kashe manufofin Amurka ne.
Ayotollah Ali Khameni yana magana kan wannan taken ne sailin da yake tattaunawa da daliban kasar, jim kadan kafin a fara bikin tunawa da ranar da aka karbe ofishin jakadancin Amurka dake Tehran a ranar 4 ga watan Nuwambar shekarar 1979.
A wannan lokacin ne dalibai masu zazzafan raayi suka tsunduma cikin harabar ofishin jakadancin na amurka suka kame Amurkawa 52 har na tsawon kwanaki 444.
Tun daga wannan lokacin nekasashen suka yanke huldan jakadanci, sai dai a zamanin wannan shugaban maici ne Hassan Rouhani yayi kokarin ganin an inganyta dangataka tsakanin kasashen biyu, ciki ko harda ma yarjejeniyar da aka cimmawa da kasar ta Iran da Amurka da kuma sauran manyan kasashen duniya.
Khameni dai ya jaddada cewa manufar taken ba yana nufin kashe Amurkawa bane, amma yana nufi kashe manufofin kasar ta Amurka da ta halin ta naji da kai.
Ana ji da wannan take a kasar Amurka