Ministan Yace ci gaba da kasancewar Al-Assad kan karagar mulki ba abinda ya damu Moscow bane.
Yace basu taba cewa ci gaba da zamowar Assad kan karagar mulki shine babban manufar su ba game da manufofin Rasha a Syria.
Mai Magana da yawun ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Maria Zakharova ta fada wa wani gidan radio jiya talata cewa kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru hudu ana yi a kasar ta Syria shine kawai zai samar da kasa ta gari da gwamnati mai aiki.
Sai dai kuma tace sake wata sabuwar gwamnati yanzu haka a kasar ta Syria kamar yadda wasu da yawan kasashen yammacin Turai ke ikirarin ayi, na iya haifar da mummunar balai a wani yankin kasar wanda hakan sai ya fi muni ga irin abiinda yakin da aka kwashe tsawon lokaci anayi
Tace sama da mutane dubu dari biyu ne suka mutu sakamakon wannan yaki na kasar Syria wanda aka fara shi tun a shekarar 2011 kuma ya ya raba miliyoyin yan kasar da muhallin su