Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Da Aka Dauka Don Dakile Masu Shirin Ta Da Rikici Ranar Rantsar Da Biden


Jami'an tsaro na musamman da aka girke a Birnin Washington.
Jami'an tsaro na musamman da aka girke a Birnin Washington.

Hukumomi a Amurka sun tsaurara matakan tsaro a birnin Washington DC yayin da ya rage kwanaki a rantsar da zababben Shugaba Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46.

Gabanin bikin rantsar da zababben shugaba Joe Biden a matsayin shugaban Amurka da za a yi a ranar 20 ga watan Janairu, jami’an tsaro a birnin Washignton DC, na ta daukan matakai domin kaucewa irin hatsaniyar da ta auku a ranar 6 ga watan nan inda dubban magoya bayan shugaba Trump suka mamaye ginin majalisar dokokin Amurka.

Jami’an tsaron da aka daurawa alhakin kula da bikin rantsar da zababben shugaban kasa, sun kuduri aniyar kaucewa aukuwar abin da ya faru a ginin majalisar dokokin kasar a makon da ya gabata – lamarin da ya kai ga zub da jini a lokacin da magoya bayan shugaba Trump mai barin gado suka yi wa majalisar kawanya.

Dubun dubatar jami’an tsaro na musamman daga jihohi za su isa birnin Washington nan da zuwa karshen makon nan.

Mai rike da mukamin Magajin Garin birnin na Washington Muriel Bowser ta ce, bikin rantsar da Biden, ya kawo wani babban kalubale da da ba a taba fuskanta ba – abin da ya kama daga matsalar annobar COVID-19 zuwa barazanr masu tsattsauran ra’ayi.

“Mutanen da za su zo don yin zanga zanga cikin lumana sun banbanta da mutanen da muka gani a ginin majalisar dokoki a ranar nan. Kuma ina ganin, za a ga cewa, mutanen da suka shiga ginin majalisar sun shirya, an kuma horar da su ne.” In ji Bowser.

A ranar Talata, hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta ce, ta samu hotunan bidiyo dubu 100 da hotuna a matsayin wani abu da aka ankarar da su a binciken da take yi inda hukumar ta ce har an bude file 160 kan mamaye ginin majalisar.

“Za mu fi mayar da hankali ne kan laifukan da suka shafi kalaman da ke tunzura jama’a. Za kuma mu tafiyar da wannan lamari daidai da yadda za mu tafiyar da ayyukan ta’addanci na kasa da kasa ko yadda muke tunkararsu. In ji Steven D’Atuono, jami’i a hukumar FBI.

Murkushe ayyukan ta’addanci na cikin gida na da wasu kalubale idan aka kwatanta da yaki da ayyukan ta’addanci a kasashen ketare.

“A nan, lamarin ya shafi haifaffun Amurkawa ne wadanda suka girma a nan. Wadanda kuma suke da kariya karkashin kundin tsarin mulki. Kuma suna sane da mafari da kuma karshen wannan ‘yanci dangane da iyakar inda za su kai kafin su shiga ajin masu manyan laifuka.” Said Javed Ali, kwararre a fannin yaki da ayyukan ta’addanci a jami’ar Michigan ya ce.

Yayin da yake amsawa wata tambaya da VOA ta yi masa a farkon makon nan, Biden ya ce, ba ya tsoron karbar rantsuwar kama aiki a waje, domin haka aka al’adar Amurka take.

“Amma ina ga, yana da muhimmanci a matukar takawa masu yin kalaman haddasa fitna birki, da wadanda suke barazana ga rayukan jama’a, su barnata dukiyar jama’a, ya kamata a kama su.” In ji Joe Biden.

Cikin tsawon makonni, hukumomi sun yi ta bibiyar shafukan yanar gizo mallakar masu tsattsauran ra’ayin mazan jiya da masu fafutukar ganin an Fifita farar fata yayin da suke kira kan harin da aka kai a majalisar dokoki a ranar 6 ga wata.

Yanzu suna mayar da hankali ne kan wadanda suke shirin ta da zaune tsaye ne gabani da kuma ranar da za a yi bikin rantsarwar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG