Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Burkina Faso Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki


Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso

Hukumomim Burkina Faso sun ce sun yi nasarar dakile wasu hare-haren ta’addancin da aka yi yunkurin kai wa a lokaci guda a wasu mahimman wuraren birnin Ouagadougou ciki har da fadar shugaban kasa.

Ministan tsaron cikin gida Mahamadou Sana da ke wannan bayani a kafar talbijan RTB ya ce jami’an tsaron Burkina Faso da hadin gwiwar takwarorinsu na Nijar sun yi nasarar kama mutane da yawa da ake zargi da hannu a wannan al’amari da aka kitsa daga kasashen Cote d’ivoire da Ghana a karshen watan Agustan da ya shige.

Yace ‘’gungun na farko da aka dora wa nauyin kai farmaki a ranar 29 ga watan Agusta wanda shine mafi girma daga cikin wadanda aka tsara na kunshe da ‘yan ta’adda 150 da ya kamata su tashi daga yankin gabas maso tsakiyar kasar don kutsawa Ouagadougou da nufin kwace fadar shugaban kasa.’’

Aikin da aka bai wa gungu na biyu shine kai farmaki a sansanin jiragen soja maras matuka don hana dukkan wani yunkurin maida martani yayinda gungu na 3 da ya fito daga Cote d’Ivoire aka ba shi aikin bude wuta a wajajen Bangodara da zimmar tarwatsa sojojin da ke wannan shiya.

Sannan wasun an bukace su su kai hari a filin jirgi don hana jiragen aminai kawo dauki.’’

Ya kara da cewa ‘’a yayin binciken da aka yi ma’aikatar tattara bayanan sirri ta sami labari jami’an tsaro sun kama wasu mutane 2 da ba su da takardu a mashigar birnin Yamai a ranar 29 ga watan Agusta.

Bayan an saurare su wadanan mutane sun bayyana cewa tare suke da wani mutum mai sunan Akushi wanda tuni ya riga su shiga Yamai kafin jami’an tsaro su kama shi a washegarin 30 ga watan Agusta a wata tashar motocin jigila ya na kokarin arcewa.

Takardun wannan mutumin sun yi nuni da cewa sunansa na gaskiya Ahmed Kinda a baya shine kwamandan rundunar sojan musamman Forces Speciales wanda ya kamata ya tafi Marocco domin daukan horo amma kuma a nan ya bayyana a matsayin jagaban dukkan hare-haren da aka tsara kaiwa. Su kuwa wadancan mutane 2 su ne Ousman Abdoulaye da Amadou Amadou Idrissa dukkansu jagororin ‘yan ta’adda.

Bayan an damkesu, Burkina Faso a bincike ta tabbatar da cewa wasu ‘yan kasar dake ketare ne ke shirya makarkashiya da nufin rikita al’amura.’’

Tuni jama’a suka fara tofa albarkacin baki game da wannan sabuwar dambarwa. 'Dan rajin kare dimokradiya kuma shugaban kungiyar fafutika ta FCR Souley Oumarou na cewa bai yi mamakin faruwar abinda hukumomomin Burkina Faso ke kira yunkurin juyin mulki ba.

Tsohon magajin garin Dori da tsohon ministan harkokin wajen Burkina Alpha Bari da wani wanda aka bayyana a matsayin mai shiga tsakani a zamanin Paul Henri Damiba da tsohon 'dan jarida Abdoulaye Bari na daga cikin wadanda aka ayyana a matsayin kusoshin wannan yunkuri.

An kuma ambato sunan wani 'dan jaridar Canal 3 wakilin sashen wasanni na BBC Serges Maturin 'dan asalin Cote d’ivoire mazaunin Nijar wanda ya yi batan dabo a ranar 31 ga watan Agusta 2024 a jerin wadanda ake zargi da hannu a wannan harka, sanarwar ta ce ya bai wa Ahmed Akushi masauki sannan ana zarginsa da kasancewa wanda zai jagoranci ayyukan tsallaka ‘yan ta’adda daga Nijar zuwa Burkina Faso.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Burkina Faso Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG