Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laifin Juyin Mulki :Kotu Ta Yanke Wa Mutane 6 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Ghana


KOTUN GHANA
KOTUN GHANA

Bayan shafe tsawon lokaci ana shari’a a babban kotun kasar, kotun ta yanke wa mutane 6 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan aka same su da laifin juyin mulki.

Wata babbar kotu a kasar Ghana ta yanke wa mutane shida, da aka samu da laifin juyin mulki, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An tuhume su da laifuffuka daban-daban, da suka hada da hada baki da cin amanar kasa, da taimakawa ga cin amanar kasa, da kuma cin amanar kasa.

Mutane shidan da suka hada da sojoji uku su ne; Donya Kafui, wanda aka fi sani da Ezor da Bright Alan Debrah Ofosu, an same su da laifin haɗa baki da cin amanar ƙasa, yayin da Johannes Zikpi (wani ma'aikacin farar hula na rundunar sojojin Ghana) aka same shi da laifin haɗa baki wajen aikata babban cin amanar kasa.

Sojoji ukun su ne – Warrant Oficer Esther Saan Dekuwine, Lance Kofur Ali Solomon, da Kofur Sylvester Akanpewon, an same su da laifin hada baki wajen aikata cin amanar kasa.

Dukkan wadanda ake zargi da hannu cikin lamarin sun musanta aikata laifin.

An jibge 'yan sanda dauke da manyan makamai a harabar babbar kotun a ranar Laraba, a yayin zaman sauraren karar da kuma yanke hukunci.

Antoni Janar din kasar Ghana Godfred Yeboah Dame wanda ya shigar da karar ya yaba da sakamakon hukuncin domin ya zama ishara ga masu niyyar aikata hakan.

ATONI JANAR GODFRED YEBOAH
ATONI JANAR GODFRED YEBOAH

"Hukuncin ishara ce mai karfi ga al'ummar kasa. Ko da wani na yunkurin ta da zaune tsaye a kasar, duk wani yunkuri na tayar da kayar baya, ba za mu lamunce hakan ba domin mun dauke shi da mahimmanci."

Sai dai babbar kotun ta wanke Kwamshinan ‘Yan Sanda, Benjamin Agordzo da jami’in soji, Kanar Samuel Kodzo Gameli da wani karamin soja, Kofur Seidu Abubakar.

Bayan yanke hukuncin, Benjamin Agbodzo ya bayyana farin ciki da godiya ga Allah, ya na mai cewa "abin farin ciki ne; godiya na ga Allah, shi kadai ya aikata hakan. Kun ji hukuncin, kuma kun ga duk abin da aka kitsa na karya, sun san ƙarya ce, amma suka ci gaba yi, suna ƙullawa, amma burinsu bai cika ba."

Lauya Anas Mohammed yace hukuncin da aka dauka ya yi daidai da dokar Ghana, domin in dai kotu ta samu mutum da laifi dumu-dumu na cin amanar kasa, kisa ne.

"A dokar Ghana, in dai kotu ta kama mutum da laifin cin amanar kasa, babu wani zabi sai hukuncin kisa. Saboda muhimmancin da aka dauki babban cin amanar kasa a dokar mu, ya sa alkalai 3 ne suke yin alkalancin shari’ar. Amma, kowace shari’a da ba ta cin amanar kasa ba, to alkali daya ne yake alkalanci." in ji Lauyan

Lauya Anas ya kara da cewa, ko da yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa akwai kisa a ciki, shekaru da dama ba a zartar da wannan hukuncin ba.

Daya daga cikin lauyoyin mutane shidan, Victor Adawudu, ya ce tawagar da ke kare wadanda ake zargin za ta garzaya Kotun Kolin kasar domin kalubalantar hukuncin.

Saurari rahoton Idriss Abdallah:

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG