Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Yi Bayani Kan Kashe Ahmed Gulak Da Aka Yi A Jihar Imo


Ahmed Gulak
Ahmed Gulak

Hukumomi a Jihar Imo, sun yi bayani game da kashe tsohon mai bai wa tsohon shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmed Ali Gulak, wanda wasu 'yan bindiga suka yi a safiyar jiya Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Imo, S.B Bala El-Kana ya yi wa Muryar Amurka karin haske akan wannan lamarin inda ya ce sun sami labarin cewa 'yan bindiga ne suka harbe shi har lahira yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga birnin Owerri a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar.

Ya kara da cewa da farko basu san shi ba ne, daga baya ne aka gano cewa shine domin basu da labarin bakwancinsa jihar.

Har yanzu dai ba'a gano ko barayi ne ko kuma su wanene suka kai wannan harin ba, amma ya ce lalle sai sun gano su.

Karin bayani akan: Gulak, jihar Imo, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

Shi kuwa Alh. Suleiman Ibrahim Sulaiman, babban mai taimakawa gwanman jihar Imo kan harkokin 'yan arewa ya ce basu ji dadin lamarin ba, kuma wadannan yan bindigan sun aikata ne don kada a sami zaman lafiya a jihar Imo.

Lamarin dai ya kara jefa jihar Imo da ke fama da matsalar tsaro cikin fargaba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG