Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harkoki Sun Tsaya A Kudu Maso Gabashin Najeriya Bayan Da IPOB Ta Bada Umarnin Zama a Gida


Wani titi a jihar Imo (Twitter/Hope_Uzodimma1)
Wani titi a jihar Imo (Twitter/Hope_Uzodimma1)

Ko da yake, jama’a sun kauracewa wuraren kasuwancin mafi yawan manyan biranen wadannan jihohi, amma an ga jami’an tsaro girke a wasu yankunan biranen suna sintiri don tabbatar da doka da oda.

Rahotanni daga yankin Kudu maso gabashin Najeriya na cewa, harkokin yau da kullum sun tsaya cak bayan wani umarni da kugiyar IPOB da hukumomi suka haramta ta bayar, na jama’a su zauna a gida a ranar Litinin a daukacin yankin.

Kungiyar wacce ke fafutukar kafa kasar Biafra, ta ba da umarnin ne don zagayowar ranar da aka kafa ta shekara 54 da suka gabata.

Jiha biyar ne a yankin, wadanda suka hada da Imo, Anambra, Abia, Enugu, da Ebonyi, kuma rahotanni sun yi nuni da cewa, jama’a da dama sun bi umarnin, lamarin da ya kassara harkokin ya da kullum.

Bayanai sun yi nuni da cewa, bankuna, makarantu, kasuwanni da kantuna a sassan yankin sun kasance a rufe, illa mutane kalilan da ke wulgawa.

Ko da yake, jama’a sun kauracewa wuraren kasuwancin mafi yawan manyan biranen wadannan jihohi, amma an ga jami’an tsaro girke a wasu yankunan biranen suna sintiri don tabbatar da doka da oda.

Yankunan kudu maso gabashin Najeriyar da dama sun fada cikin rudani a ‘yan kwanakin nan, inda aka yi ta ganin hare-haren da ake zargin ‘yan bindigar kungiyar IPOB da kai wa, wadanda ke kaikaitar ofisoshin ‘yan sanda da ma’aikatun gwamnatin jiha da na tarayya.

Karin bayani akan: Ahmed Gulak, jihar Imo, APC, PDP, Goodluck Jonathan, IPOB, Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Al’amura sun fi rincabewa a jihar Imo, wacce ko a karshen makon da ya gabata, sai da ‘yan bindiga suka kashe Ahmed Ali Gulak, tsohon mai ba tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha’anin siyasa.

A Lahadi, rundunar ‘yan sanda jihar ta Imo ta ce ta harbe ‘yan bindigar da suka kashe Gulak tare da kwato wasu makamai da motoci.

Al’amuran tsaro da suka rincabe a wadanda yankuna, sun yi tasiri kan harkokin kasuwancin jihohi musamman birnin a Owerri na jihar Imo.

XS
SM
MD
LG