Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe Barrister Ahmed Gulak, tsohon mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha’anin siyasa.
Ayyuba Gulak, kani ga marigayin, ya tabbatarwa da Muryar Amurka rasuwar dan uwan nasa ta wayar tarho.
Da safiyar ranar Lahadi jaridun Najeriya da dama suka ruwaito cewa an kashe Gulak ne yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga birnin Owerri na jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a cewar rahotannin.
Wasu majiyoyi da gidan talabijin na Channels ya yi hira da su, sun ce ‘yan bindigar sun bi sahun Gulak ne tun daga otel din da ya sauka zuwa inda suka harbe shi a lokacin yana hanyarsa ta zuwa filin tashin jirage.
Karin bayani akan: Ahmed Gulak, jihar Imo, APC, PDP, Goodluck Jonathan, IPOB, Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari,, Nigeria, da Najeriya.
Gulak tsohon kakaki ne a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
A watan Fabrairun shekarar 2018, Barrister Gulak ya sauya sheka ya koma APC tare da wasu gaggan jam’iyyar da magoya bayansu sama da 40,000.
“Lokaci ya yi da za mu yi rijista a matsayin mambobin APC. Lokaci ya yi da za mu binne PDP a Adamawa.” Gulak ya ce a wajen gangamin karbarsu, wanda aka yi gabanin wata ziyara da Shugaba Muhammadu Buhari, ya kai jihar a lokacin.