‘Yan bindiga sun sace daruruwan daliban makarantar Islamiyya a Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar Nejan Najeriya.
Lamarin ya faru ne a makarantar Salihu Tanko Islamic Primary and Nursey School.
Sakataren gwamnti kuma shugaban kwamitin kula da harkokin tsaron jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatarwa da Muryar Amurka aukuwar wannan lamari.
Amma ya ce har yanzu ba su kammala tantance iya adadin daliban da aka sace ba.
Matane ya yi kira ga iyayen daliban da su tuntubi hukumomin jihar domin a san iya adadin daliban da ‘yan bindigar suka kwasa.
Rahotanni da dama sun ce daliban da aka sace a makarantar wacce ta maza da mata ce sun kai 200.
A karin hasken da ya yi, Alhaji Isma’ila Modibbo, ya tabbatarwa da Muryar Amurka sace daliban makarantar ta Islamiyya.
A tsakiyar watan Fabrairu, ‘yan bindigar suka sace dalibai 27 makarantar kwana da ke Kagara a jihar ta Neja, wacce ke tsakiyar arewacin Najeriya
An sako daliban bayan da suka kwashe wani tsawon lokaci a hannun 'yan bindigar.