July 4 (Reuters) - An kashe mutane 10 kana wasu 38 sun jikkata a sakamakon wani harin mai kan uwa da wabi da aka yi a Philadelphia da Baltimore da kuma Fort Worth gabanin bukin ranar ‘yancin kan Amurka da akayi a ranar Talata, 4 ga watan Yuli a cewar jami'ai, lamarin da ya haifar da sabbin kiraye-kiraye ga shugaban Amurka Joe Biden na samar da dokar mallakar bindigogi.
kamfanin dillancin labarai na reuters ya ruwaito cewa a Fort Worth, ‘yan sanda sun sanar cewa an kashe mutane uku yayin da mutum 8 suka jikkata a harbin mai kan uwa da wabin da aka yi dan murnar zagayowar ranar ‘yancin Amurka.
Banda wannan, a wani harbin da akayi a Philadelphia a ranar Litinin da yamma kuma, an kashe wasu mutane 5, kana wasu mutum biyu sun jikkata cikin su har da wani dan yaro mai shekaru 2 da wani mai shekaru 13 a duniya dukkanin su an harbe su a kafa, a sa’ilin da wani da ake zargi sanye da sulke da kuma bindiga samfirin AR-15 ya bude wuta akan mutanen da bai sansu ba, a bisa bayannan ‘yan sanda.
Harbin na ranar Litinin, ya biyo bayan da wasu mutane biyun da aka budewa wuta suka mutu sannan wasu 28 kuma suka jikkata, wanda kusan rabin su yara ne a wani harbin da akayi a wurin wani buki a cikin wata unguwa a birnin Baltimore.
Ya zuwa yanzu dai ba tabbatar da musabbabin wadannan harbe-harben ba, Amurka dai tana fama da matsalar yawan harbe-harben mai kan uwa da wabi da kuma rikice-rikicen matsalolin da suka shafi tashin hankali da bindiga.
Ya zuwa yanzu, an samu matsalolin harbe-harbe har sau 340 a cikin wannan shekarar ta 2023 a kasar, bisa alkaluman da aka tattara daga kundin addana bayanan tashe-tashen hankula da bindigogi, kundin da ya bayyana harbin mai kan uwa da wabi a matsayin wanda aka harbi akalla mutane 4 ba tare da lissafa shi mai harbin a cikin wannan lisafi ba.
Shugaba Biden ya yi Allah wa dai da tashin hankalin na ranar Talata kana ya dada jaddada anniyar sa na yiwa dokar mallakar bindiga a Amurka garambawul.