Sai dai hukumomin sun sanar da kama dan bindigar da ake zargi.
Hukumar binciken manyan laifuffuka ta jihar Georgia ta bayyana cewar an kashe mutane 4, sai dai kai tsaye bata bayyana dalilin da ya sabbaba aikata hakan ba.
Sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ya bayyana cewa, “an garzaya da karin wasu mutanen 9 zuwa asibiti dauke da raunuka. Wanda ake zargi na tsare a hannun hukuma da ran sa. Babu kamshin gaskiya a rahotannin dake cewa an kashe shi.”
Tun da fari, an samu rahoton cewa hukumomin makarantar sun aikewa iyayen dalibai da sakon cewar suna aiwatar da “wata tsatsaurar dokar hana zirga-zirga tun bayan samun rahoton bude wutar.”
Dandalin Mu Tattauna