Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyu Sun Jikkata Sakamakon Harin Harbi A Wata Babbar Coci A Texas


Cocin Joel OSteen
Cocin Joel OSteen

An harbe wani yaro dan shekara biyar kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti," a cewar shugaban 'yan sandan birnin Houstan, yayin da wani mutum ke jinyar harbin bindiga a kafa.

Wasu mutane biyu, ciki har da wani yaro dan shekara biyar sun jikkata bayan da wata mata ta bude wuta kan wata babbar cocin fitaccen Paston da ake kira Joel Osteen a birnin Houston da ke jihar Texas a Amurka, daya daga cikin wuraren ibada mafi girma a kasar, a cewar 'yan sanda ranar Lahadi.

Matar dai na dauke da bindiga a lokacin da ta shiga cocin tare da wani yaro kusan karfe 2:00 na rana agogon GMT, kamar yadda shugaban ‘yan sandan Houston Troy Finner ya shaida wa taron manema labarai.

A lokacin da ta isa cocin, wacce a da babban filin wasanni ce da mutane kusan 16,800 ke taruwa a cikinta, ta fara harbi, in ji Finner, amma jami'an 'yan sanda da ke aikin tsaro a wurin suka harbe ta har lahira.

Joel Osteen
Joel Osteen

"An harbe wani yaro dan shekara biyar kuma yana cikin mawuyacin hali a asibiti," in ji Finner, yayin da wani mutum mai shekaru 50 na jinyar harbin bindiga da ya samu a kafa.”

Hare-hare kan jama'a sun zama ruwan dare a Amurka, inda ake da bindigogin da suka fi jama’a yawa kuma kusan kashi uku na Amurkawa manya sun mallaki bindiga.

Osteen, wanda ake watsa shirye-shiryen sujada a cocinsa kai tsaye ga miliyoyin mutane a duk mako, kuma wanda bai tsoma cocin cikin harkokin siyasa, ya ce harin ya “tada masa hakalinsa sosai.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG