Wani curin dutse dake rikidewa ya zamo tauraruwa mai wutsiya idan ya shigo samaniyar duniyar dan Adam, wanda kuma girmansa ya kai jirgin ruwan yaki na dakon jiragen sama, ya wuce ta kusa da duniya a wani abinda masana suka ce shi en tarkacen samaniya mafi girma da ya kusanto duniyarmu cikin shekaru fiye da talatin.
Wannan curin dutsen samaniya mai suna YU55, ya zo wuri mai tazarar kilomita dubu 325 daga doron duniya da karfe 12 da minti 28 na daren da ya shige. Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, wadda ta auna hanyar da wannan dutse ke bi, ta ce ba zai fado kan duniya ko kuma a kan wata ba. Wannan curin dutse yana tafiyar kilomita dubu 46 da 670 cikin kowace awa daya.
Rabon da curin dutse mai zamowa tauraruwa mai wutsiya mai girma wannan ya zo kusa da duniyar bil Adama tun 1976. Masana kimiyya suka ce sai a shekarar 2028 ne wani curin dutsen daga samaniya zai sake kusantar duniyarmu.
Wani masanin kimiyya a jami’ar Arizona shi ne ya gano wannan curin dutse mai suna YU55 a shekarar 2005.
Shi dai wannan curin dutse yana da fadin mita 400. Masana kimiyya sun yi imanin cewa ya sha wucewa ta kusa da duniyar bil Adama dubban shekaru da suka shige.