Kungiyar agajin jin kai da taimakon gajiyayyu ta Red Cross ko Croix Rouge tace mutane 63 a kalla sun mutu a arewacin Najeriya bayan wasu jerin fashewar boma-bomai da harbe-haebe a garin Damaturu na jahar Yobe.
‘Yan bindiga sun kaiwa garin hari da yammacin jiya Jumma’a, su ka farfasa boma-bomai a ofisoshin ‘yan sanda, da wani banki da kuma Coci-Coci da dama. An kwan dare ana barin wuta a garin, har ya zuwa safiyar yau asabar.
Haka kuma ‘yan bindigar sun kai hari kan wani kauyen da ke Poktiskum, inda suka kashe mutane biyu a cewar shaidun gani da ido.
Babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare. Amma mazauna yankin sun dora laifin a kan ‘yan Boko Haram wadanda suka sha kai hare-hare a arewacin kasar ta Najeriya.
Har yanzu gwamnati ba ta ce komi ba akan wadannan hare-hare.
Hare-haren na yammacin Jumma’a a garin Damaturu sun wakana ne bayan tashin dimbin boma-bomai da safe a garin Maiduguri da ke kusa da Damaturu. Mutane da yawa sun ji ciwo, amma har yanzu babu tabbas game da adadin wadanda suka mutu a cikin harin.
Duka wadannan hare-hare na Maiduguri da Damaturu sun wakana a cikin watan Dhul-Hijjah, ana sauran kwana biyu a yi sallar layya.