Sakamakon matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihar Tilabery, rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun kona motocin dakon itace sama da 40 dauke da lodin iccen a jejin iyakar Nijar da Burkina Faso da kuma Mali.
A wata sanarwar da suka fitar domin ankarar da mahukunta da ma al’umma abinda suka kira halin kuncin da matsalolin tsaro suka jefa direbobin motocin dakon itacen girke-girke, shugabannin kungiyar ANEB sun fayyace yanayin da wannan aiki ke gudana tun bayan tsanantar aika-aikar ‘yan ta’adda a yankin da ake yi wa lakabin iyakar kasashe uku, kamar yadda babban sakataren kungiyar ya bayyana.
Wannan matsala ta haddasa dimbin asarar da girmanta ya haura daruruwan miliyoyin CFA a cewar magatakardan kungiyar ANEB.
Kasuwancin itacen girke-girke dadaddiyar sana’a ta gadin-gadin wata hanya ce ta samar da makamashi da mafi yawancin jama’ar Nijar ke dogaro a kanta, hatta ‘yan shekarun nan da kasar ke sayar da iskar gas dinta a kasuwanni, a saboda haka wani jigo a kungiyar fafutukar samar da wadatar makamashi CODDAE, injiniya Rabiou Malan issa, ke gargadin hukumomi akan bukatar daukar mataki domin a cewarsa shi ganau ne.
Kungiyar ta ANEB ta ce ta aike da wasiku ga fadar Firai Minista da wasu ministocin da ke kula da wannan fanni akan bukatar neman mafita sai dai kawo yanzu ba ta sami amsa daga garesu ba.
Saurari rahoton Souley Mumuni Barma: