A ranar biyar ga watan bakwai na shekarar bara ne dai 'yan-bindiga su ka afkawa makarantar Bathel Baptist dake Damishi a jahar Kaduna, inda su ka sace dalibai 121.
'Yan-bindigan dai sun dinga sakin daliban ne da kadan-kadan har yanzu karshen shekarar bara sai dai shugaban kungiyar Kiristochi ta Kasa reshen jahar Kaduna, Rabaren Joseph John Hayeph ya ce har yanzu akwai sauran dalibin da ba a saki ba.
Afkawa makarantu da 'yan-bindiga su ka dinga yi a wasu makarantun jahar Kaduna dai ya bar wani wagegen gibi a bangaren ilimi domin da yawan iyaye sun shiga rudani game da barin yaran su zuwa makaranta, inji shugaban kungiyar malamai da iyayen yara ta Kasa, Alh. Haruna Danjuma.
Duk da fargabar tsaro da aka gani a makarantu bara, masani kan harkokin tsaro, Manjo Muhammadu Bashir Shu'aibu Galma mai ritaya ya ce akwai alamun sauyi bana.
Barkawa wasu daga cikin dajujjukan da jami'an tsaro su ka yi dai ya kawo saukin hare-haren 'yan-bindiga a wasu sassan jahar Kaduna ko dake ko a jiya Talata sai da gwamnatin jahar ta sanar da kashe wasu mutane da 'yan-bindigan su ka yi a yankin karamar hukumar Igabi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: