Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Wasu Ɗaliban Makarantar Bethel Biyu da Aka Sace


Wani mahaifi da ya karbi 'yarsa bayan da aka sako daliban Bethel
Wani mahaifi da ya karbi 'yarsa bayan da aka sako daliban Bethel

Wasu karin dalibai biyu da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna sun samu ‘yancinsu.

Duk da cewa har yanzu hukumomin ‘yan sanda ba su ce uffan ba kan lamarin, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Reverend Joseph Hayab ya ce an sako daliban biyu ne a ranar 28 ga Disamba, 2021, da kuma ranar 1 ga watan Janairu. 2022, bi da bi.

A ranar 5 ga Yuli, 2021 ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Maraban Damishi, a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da dalibai 121.

Daga baya an sako daliban a hankali a hankali bayan da aka ce iyayensu sun biya kudin da ba a tantance adadinsu ba a matsayin kudin fansa yayin da wasu uku suka rage a hannun barayin.

Da sakin daliban biyu, adadin dalibai 120 ne suka samu ‘yancinsu ya zuwa yanzu yayin da dalibi daya kacal ke hannun garkuwa

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG