Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Biya Kudin Fansa Wajen Karbo Daliban Bethel Ba - Rev. Akanji


Wasu daga cikin iyayen daliban Bethel da suka karbi 'yarsu a ranar Lahadi
Wasu daga cikin iyayen daliban Bethel da suka karbi 'yarsu a ranar Lahadi

Shugaban kungiyar Kiristoci ta jihar Kaduna, Rev. Joseph John Hayeph ya ce babu hannun gwamnati a kokarin karbo wadannan dalibai.

Shugaban Mujami’ar Baptist a Najeriya, Rev. Dr. Israel Akanji ya ce biyan kudin fansa ba ya cikin abubuwan da suka yi wajen ceto daliban makarantar Bethel Baptist da aka sace a jihar Kaduna a farkon watan Yuli.

A ranar Lahadi 25 ga watan Yuli aka sako karin wasu dalibai 28.

“Mun samu kiran waya, inda aka ce mana mu je wuri kaza za mu same su, mun sha samun haka, idan mun je ba za mu samu komai ba, amma a wannan lokaci da muka je, mun samu ‘ya’yanmu 28 kuma mun debo su mun zo da su.” In ji Rev. Akanji, wanda ya halarci wajen taron mika yaran ga iyayensu.

Wani mahaifi da ya karbi 'yarsa bayan da aka sako daliban Bethel
Wani mahaifi da ya karbi 'yarsa bayan da aka sako daliban Bethel

A cewar Rev. Akanji, ba a biya kudin fansa wajen kubutar da daliban ba.

“Biyan kudin fansa ba ya cikin abubuwan da muka yi, mun dogara ga Allah, mun yi ayyukan da muka iya.”

Shugaban kungiyar Kiristoci ta jihar Kaduna, Rev. Joseph John Hayeph ya ce babu hannun gwamnatin a kokarin karbo wadannan dalibai.

“Da mu masu coci, da iyayen yara, da kuma shugabanninmu na kungiyoyin Kiristoci na Najeriya da shugabannin Baptist a ko ina a Najeriya, tare muka yi kokari don mu ga an ceto yaran nan, gwamnati ba su da hannu, baa bin da suka yi, ai yaran nan ba yaran gwamnati ba ne, yaran talakawa be.” In ji Rev. Hayeph.

Daya daga cikin daliban da aka karbo
Daya daga cikin daliban da aka karbo

Rev. Hayeph ya kara da cewa, yanzu haka akwai sauran dalibai akalla 87 a hannun ‘yan bindigar.

Kokarin jin ta bakin gwamnati ya ci tura, amma a baya, hukumomin jihar ta Kaduna sun dauki matsayar cewa ba ta amince da biyan ‘yan bindiga kudin fansa ba ko kuma yin sulhu da su.

Akalla dalibai 121 ‘yan bindiga suka sace a makarantar ta Bethel wacce ke karamar hukumar Chikun a jihar Kadunan da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar 8 ga watan Yuli.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG