Rahotanni daga Najeriya na cewa an saki wasu daga cikin daliban Bethel Baptist Church da aka sace a farkon watan Yuli a Jihar Kaduna da ke Arewa maso yammacin kasar.
Bayanai sun yi nuni da cewa da sanyin safiyar ranar Lahadi aka tsinci dalibai 28 a dajin da ake kira tsoho gaya a jihar.
‘Yan bindigar da suka sace daliban 121 a ranar 8 ga watan Yuli sun nemi a biya dubu 500,000 kan kowanne dalibi a matsayin kudin fansa.
Sai dai babu wasu bayanai da ke nuna cewa kudin fansa aka biya aka sako wannan tawagar daliban ko akasin haka.
Bugu da kari, babu rahotanni da suka nuna ko kubutar da su jami’an tsaro suka yi ko kuma tserewa suka yi da kansu.
A kwanankin baya an saki uku daga cikin daliban makarantar ta Bethel Baptist Church wacce ke karamar hukumar a Chikun da ke jihar ta Kaduna.
Wani hoton bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da ake mika yaran ga iyayensu, ko da yake, Muryar Amurka ba ta tantance sahihancin bidiyon ba.