Hannayen jari a kasuwannin duniya sun fadi yau litinin sakamakon rage cancantar ba Amurka bashi na kasa da kuma damuwa da ake nunawa dangane da matsalar basuka a kasashen turai. Hannayen jari a kasuwannin Amurka sun fadi da misalin kashi 2% yau da safe. Manyan kasuwannin hannayen jari na kasashen duniya sun fadi da kimanin kashi 4% a lokacin rufe kasuwannin, yayinda hannayen jari na kasashen turai suka fadi da sama da kashi 2% yau da rana. Cinikayyar yau Litinin da safe ne dama ta farko da masu zuba jari da dama suke da ita ta bayyana ra’ayoyinsu dangane da rage cancantar ba Amurka bashi da aka sanar ranar jumma’a da yamma bayan rufe kasuwannin hanayen jari. Matsayin cancantar ba Amurka bashi ya ragu karon farko zuwa maki biyu a maimakon matsayinta na uku da yake nuna kyakkyawar cancanta. Cibiyar tantance cancantar ta kira taro yau Litinin domin kare kanta kan dalilanta na yanke wannan hukumcin.
Manajin darektan cibiyar S & P John Cambers shugaban kwamitin da ya yanke wannan hukumcin yace kara bashin dake kan Amurka da kuma kasa cimma yarjejeniya tsakanin shugaban kasa da majalisa kan gagarumin rage gibin kudi sun sabawa matsayin cancantar bada bashi na zamanin gwamnatocin da suka sami wannan maki. Shugabannin Amurka sun kushewa rage matsayin cancantar cin bashin, wanda ke nuni da cewa, cibiyar ta hakikanta sayen kaddarorin gwamnati na bond yanzu kasada ce. Sakataren baitulmalin gwamnatin Amurka Timothy Geithner yace cibiyar tayi kuskure da ta rage matsayin cancantar ba Amurka bashi, bisa ga cewarshi, cibiyar ta nuna gagarumar rashin fahimtar yadda ake tsara kasafin kudin gwamnati