Jiya Alhamis kasuwannin sayar da hannayen jari a Amurka da Turai sun fadi sosai sabo da an fara fargabar tattalain arzikin Duniya ya fara nuna alamun koma baya.
A Amurka, kasuwar hannayen jari ta Dow Jones ta fadi da maki 513 ko kashi 4.3 faduwa mafi girma da kasuwar ta gani tun cikin watan Okotoban 2008. Haka kuma kasuwnanin NASDAQ da wacce ake kira S&P 500 suma sun fadi.
Masana tafarkin tattalin arzikin sun ce masu zuba jari suna tsoron watakil tattalin arzikin Amurka ya tasamma ko mada.
Faduwar hannayen jari a Amurka yazo dai dai lokacinda kasuwannin hannayen jari a Turai suma suka nosa da kamar kashi hudu.
Har babban bankin turai ya bada sanarwar cewa yana ci gaba da sayen takardun baitul mali daga gwamnatoci dake kungiyar domin sassauta musu matsalolin bashi, wadda ya sa masu zuba jari suke bayyana tsoron hakan sai iya taba kasashe masu tattalin arzikin dake karfi kamar Italiya da Spain.