‘Yan takarar shugabancin Amurka a tutar Republican sunyi muhawara a jihar Iowa dake tsakiyar Amurka, da nufin tsuma magoya bayansu, gabannin gudanar da zabe na gwaji a jihar ta IOWa, domin gano wadanda suka fi karfi da karbuwa a zaben share fage, a zaben shugaban kasa da za a yi badi.
‘Yan takara takwas ne suka kara a muharawar da aka nuna kai tsaye ta talabijin daga harabar jami’ar Iowa dake birnin Ames.
‘Yan takarar sun hada da tsohon gwamnan Massachussetts Mitt Romney, wanda yake kan gaba ahalin yanzu, ‘yar majalisar wakilai ta tarayya Michelle Bachman, kuma shugabar ‘yan rikau reshen Tea Party a majalisar.
Haka kuma cikin wadanda suka shiga muhawarar har da tsohon Gwamnan Minnesota Tim Pawlenty, da kuma wakili a majalisar wakilai Ron Paul, da kuma tsohon jakadan Amurka a China Jon Huntsman. Da kuma wani bakar fata dan kasuwa.
Mutuminda bai shiga muhawarar ba shine Gwamnan jihar Texas Rick Perry, wadda ake sa ran zan bayyana niyyar takarar shugabancin Amurkan gobe Asabar idan Allah ya kaimu.