Babban jirgin ruwan yaki na China irinsa na farko da kasar zata mallaka mai daukan jiragen yaki, ya bar harabar kamfanin da yayi aiki akansa cikin kasar.
Laraban nan ne katafaren jirgin da aka kera a jamhuriyar tsohuwar Soviet, kuma aka sake yi wa kwaskawarima, ya bar gabar ruwan Dalian dake arewa maso gabashin China.
Jami’ai suka ce shirin gwajin jirgin yana tafiya kamar yadda aka tsara, kuma daga bisani jirgin zai koma kamfani inda za a ci gaba da aiki akansa.
An fara nuna damuwa kan China gameda mallakar makamai, lokacinda ta sayi jirgin daga Ukraine a 1998, bayan an kwance galibin muhimman kaya dake cikinsa. Ma’aikatar tsaron China ta fada cikin watan jiya cewa za a yi amfani da jirgin ne wajen aikin horasda jami’anta, da kuma bincike.
Ranar talata kamfanin dillancin labaran kasar, Xinxua ya buga hotunan dakunan saukar shugaban kasa biyu a cikin jirgin, da aka sake kawatawa.
Tun fil azal an kera jirgin ne a jamhuriyar Soviet, amma ba a gama aiki ba har jamhuriyar ta wargaje a 1991. Daga bisani aka mika jirgin ga Ukraine, wacce ta sayarwa China, amma sai bayan da aka cire dukkan kayan aiki dake cikinsa.