Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rage Martabar Amurka A Fagen Rance Ya Shafi Kasuwannin Duniya


Sam Rainsy, president of the Cambodia National Rescue Party (CNRP), visits a polling station during the general elections in Phnom Penh, July 28, 2013.
Sam Rainsy, president of the Cambodia National Rescue Party (CNRP), visits a polling station during the general elections in Phnom Penh, July 28, 2013.

Harkoki sun ragu kwarai a kasuwannin saida hannayen jari a kasa da kasa a zaman maida martani ga matakin da kasuwar hada-hada da jeranta karfin hannayen jarin Amurka ta SP ta bada

Harkoki sun ragu kwarai a kasuwannin saida hannayen jari a kasa da kasa a zaman maida martani ga matakin da kasuwar hada-hada da jeranta karfin hannayen jarin Amurka ta S&P ta bada sanarwar dauka wajen zaftare darajar karfin ruwan bashin da Amurka ke dashi.

Kididdigar da manyan kasuwannin hannayen jari a kasashen Asiya irin su Tokyo, da Hong Kong, da Seoul da kuma Sydney suka bayar, sunyi kasa da kusan kashi guda daga cikin dari zuwa kashi uku a budewar cinikayyar safiyar yau Litinin.

Kazalika,hannayen jarin masana’antu a birnin New York sun yi kasa tun ma kafin bude kasuwar shunkun “Wall Street”.

An kuma rufe kasuwannin hannayen jarin yankin gabas na tsakiya na karamin lokaci jiya lahadi, bayan da farashin hannayen jari suka fara yin kasa da kashi bakwai daga cikin dari a kasuwar shunkun birnin Tel Aviv.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG