Shugaban Amurka Barack Obama zai shirya liyafar bude baki ta iftar a Fadar White House a yau Laraba don, karrama watan azumin Ramadan, mai tsarki ga Musulmi.
Fadar ta White House t ace wadan da aka gayyata sun hada da shugabannin Musulmi da ‘yan gwagwarmaya da shugabannin siyasa da kuma shugabanin wasu addinai.
A watan Ramadan dai Musulmi kan yi azumi ne a rana. Iftar shi ne bude bakin da akan yi bayan azumin.
Shugaba Clinton ne ya fara wannan al’ada ta yin bude baki a Fadar White House, kuma Shugaba George W. Bush ya bi sahu. Wannan shi ne karo na uku da shugaba Obama ya shirya bude-bakin na Iftar.
A sakonsa na Ramadan na ran daya ga watan Agusta, Shugaba Obama ya bayyana fatan alheri ga al'ummar Musulmin da ke Amurka da ma duniya baki daya.
Ya kuma yi amfani da damar wajen kiran da a kara tura gudunmowa ga mutanen Somaliya da ke mutuwa da yunwa, ya na mai cewa Ramadan lokaci ne mai tuni da muhimmancin taimakawa marasa galihu.