Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Ce Har Yanzu Akwai Sarkakkiya A Tattaunawar Sulhun Gaza Duk Da Rahotannin Samun Ci gaba


Sarkin Egypt Abdel Fattah al-Sisi da Sarkin Qatar Emir Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani da Sakatare Janar na Arab League Ahmed Aboul Gheit a Cairo, lokacin tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas
Sarkin Egypt Abdel Fattah al-Sisi da Sarkin Qatar Emir Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani da Sakatare Janar na Arab League Ahmed Aboul Gheit a Cairo, lokacin tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas

Wani jami'in Hamas ya ce a ranar Litinin din nan ba a samu wani ci gaba ba a sabon zama na shawarwarin tsagaita wuta a Gaza a birnin Cairo, taron da kuma ya samu halartar tawagogin Isra'ila, Qatar da kuma Amurka, jim kadan bayan da majiyoyin Masar suka ce an cimma matsaya kan ajandar da aka daukaka

WASHINGTON, D. C. - Manyan kasashen yammacin duniya sun bayyana bacin ransu kan abin da suke gani wanda ba za a amince da shi ba na adadin fararen hula Falasdinawa da ake kashewa da kuma ‘yan jinkai a Gaza wanda ke faruruwa daga hare-haren da sojojin Isra'ila ke kai wa don neman halaka kungiyar Hamas a Gaza mai dimbin jama'a.

Mideast Egypt US
Mideast Egypt US

Isra'ila da Hamas sun aike da tawagogi zuwa Misira a ranar Lahadin da ta gabata bayan isowar darektan hukumar leken asiri ta CIA William Burns a ranar Asabar, wanda kasancewarsa ya yi nuni da karuwar matsin lambar Amurka kan yarjejeniyar da za ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma samun agaji ga fararen hula.

Jami'in Hamas wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Babu wani sauyi a matsayin mamaya saboda haka babu wani sabon abu a tattaunawar Cairo."

Williams Burns
Williams Burns

"Babu wani ci gaba tukuna."

Watanni shida da fara kai hare-hare kan kungiyar Hamas da Falasdinawa da ta yi kaca-kaca da Gaza tare da barin mafi yawan al'ummarta miliyan 2.3 ba su da matsuguni tare da fuskantar barazanar yunwa, Isra'ila dai ta kuma bayyana kyakkyawan fata game da tattaunawar ta baya bayan nan.

A birnin Kudus a karshen mako, ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katz, ya bayyana tattaunawar da aka yi a birnin Cairo a matsayin mafi kusancin bangarorin da suka cimma matsaya tun bayan wata yarjejeniyar da aka cimma a watan Nuwamba, inda Hamas ta sako da mutane da dama da suka yi garkuwa da su.

Majiyoyin tsaron Misira guda biyu da kuma Al-Qahera News sun ce an samu ci gaba a tattaunawar ta Cairo.

Shugabannin Daular Larabawa
Shugabannin Daular Larabawa

Majiyoyin tsaron sun ce bangarorin biyu sun yi rangwame da zai taimaka wajen samar da hanyar sasantawa wadda kamar yadda aka tsara a tattaunawar da ta gabata za ta kasance cikin matakai uku, tare da sakin duk wasu ‘yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su, da kuma tsagaita bude wuta na dogon lokaci a mataki na biyu.

Yarjejeniyar ta shafi kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma bukatar Hamas na mayar da mazauna yankin arewacin Gaza, in ji su.

Tawagogin sun bar birnin Cairo kuma ana sa ran ci gaba da tuntubar juna cikin sa'o'i 48, in ji majiyoyi da Al-Qahera.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG