Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Da Netanyahu Sun Fara Hararar Juna Bayan Kudirin MDD Kan Tsagaita Wuta A Gaza


Biden-Netanyahu, Tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
Biden-Netanyahu, Tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

WASHINGTON, D. C. - Ba zato ba tsammani Netanyahu ya yi watsi da wani shirin ziyara da wata babbar tawaga za ta kai birnin Washington a cikin wannan mako domin tattaunawa kan barazanar da Isra'ila ke fuskanta a kudancin birnin Rafah na Gaza, bayan da Amurka ta kaurace wa kuri'ar da kwamitin sulhun ya kada na neman tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas da kuma sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su daga mayakan Falasdinawa.

Biden-Netanyahu
Biden-Netanyahu

Dakatar da wannan taron ya sanya sabon cikas ga kokarin da Amurka ke yi, da kuma nuna damuwanta game da bala'in jin kai da Gaza ke fuskanta, don neman Netanyahu ya yi la'akari ya nemi wasu hanyoyi daban maimakon mamaye Rafah, wuri na karshe da ke zaman mafaka ga Falasdinawa fararen hula.

Barazanar irin wannan farmakin ya kara takun saka tsakanin dadeddiyar kawancen Amurka da Isra'ila, kuma ya sanya ayar tambaya kan ko Amurka za ta iya takaita taimakon soji idan Netanyahu ya ki jin ta Biden ya kuma cigaba da farmakin.

Sojojin Isra’ila kusa da iyakar
Sojojin Isra’ila kusa da iyakar

"Wannan ya nuna cewa amana tsakanin gwamnatin Biden da Netanyahu na iya rugujewa," in ji Aaron David Miller, tsohon mai shiga tsakani a Gabas ta Tsakiya na gwamnatocin Republican da Democrat. "Idan ba a kula da rikicin a hankali ba, abin zai ci gaba da tabarbarewa."

Matakin da Biden ya yanke na kaurace wa kada kuri’a a Majalisar Dinkin Duniya, ya zo ne bayan watanni da yawa na bin manufofin Amurka da suka dade suna bawa Isra'ila kariya a kungiyar ta duniya, da alamar nuna rashin jittuwa da Amurka ga shugaban Isra'ila.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG