Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadiman Danbaba Suntai Sun Ki Barin Fadar Gwamnati


Gwamnan Jihar Taraba, Mr. Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Mr. Danbaba Suntai

A wani yanayi mai kama da wasan kwaikwayo, hadiman gwamnan Taraba Mr. Danbaba Suntai wanda aka komo da shi gida fiye da makonni biyu da suka wuce, na cigaba da kin amincewa da matakan da ‘yan majalisar dokokin jihar suka dauka, na cewa Mr. Suntai ya koma jinya, domin mataimakinsa ya cigaba da jan ragamar jihar, a matsayin mukadashi har sai ranar da gwamnan ya samu sauki.

Yayin da manyan jami’an gwamnati, da sauran kwamishinoni ke cigaba da aikinsu a sakatarian gwamnatin jihar, hadiman gwamnan sun tare a gidan gwamnan tare da nada tsohon kwamishinan shari’a na jihar Barrister Gibbon Timothy a matsayin sakataren gwamnati na bangarensu.

Sai dai kuma sakataren watsa labaran mukadashin gwamnan jihar Mr. Keffers Sule yace gwamnati daya ake dashi a jihar a hukumance a karkashin jagorancin Alhaji Garba Umar kamar yadda doka ta tanada.

Wannan na zuwa ne a lokacin da kungiyoyi, da sauran al-umma na kira a kai zuciya nesa domin cigaban jihar Taraba.

Mukadashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar ya yaba wa mutanen jihar Taraba saboda kai zuciya nesa da sukayi, sannan ya bayanna aniyar cike gurbin gwamnonin da aka kora kwanaki sakamakon badakalar kudin tallafin ambaliyar ruwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG