Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gyara Kayanka Bashi Zama Sauke Mu Raba


Dalibai Masu zanga zanga a Jami'ar Calabar 12, ga Oktoba 2015
Dalibai Masu zanga zanga a Jami'ar Calabar 12, ga Oktoba 2015

Tsarin demokaradiya ya bayar da damar saka ido akan duk masu mulki, da nuna musu kura kuran su don su gyara, ta kuma baiwa al’umma damar fadin albarkacin baki kan duk abinda suke so a kasa.

Sai dai kuma akan samu wasu mutane da shugabanni dake bahagurar fahimtar cewa duk masu sukan lamirin gwamnati, ko sukan shugaba don neman ya gyara lamuran sa, sai kawai a fara kallon sa a matsayin dan adawa, ko abokin gaba, kai harma ana daukan irin wadannan mutane masu fadin albarkacin bakin su a matsayin makiyan shugaba da gwamnatinsa.

Kan wannan batu ne muka tuntubi Dakta Ahmad Abubakar, mai fashin baki da sharshi akan abubuwan yau da gobe, domin jin tsokacinsa game da wannan batun. Dakta Ahmed, yayi tsokaci kan muhimmancin tabuka abin kirki ga shugbanni alokacin da suke kan karagar mulki, inda ya bada missali da shugaba Buhari kan yadda alokacin da yake mulki mutane ke ganin yana takurawa ne ba aiki ba.

Sai bayan da akayi juyin mulki Najeriya ta sami sabbin shugabanni, sannan aka fara ganin ayyukan da Buhari yayi a lokacin da yake mulki, wanda hakan ne ya kara masa daraja a idanun mutane har suka yarda da shi suka zabe shi a matsayin shugaban kasa a mulkin farar hula.

Saurari Dakta Ahmad Abubakar don karin bayani.

XS
SM
MD
LG