Mai dakin shugaban Amurka Michelle Obama ta nuna nata goyon bayan akan dandalolin sada zumunci, inda ta saka hoto akan Facebook da Twitter, a cikin hoton akwai sakon da ke cewa tana taya iyalen daliban jimami, kuma tana yiwa yaran addu’a.
Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton itama ta tofa albarkacin bakinta game da wannan lamari wanda ya jawo hankalin duniya.
Larabannan Sojin Amurka tace masu bada shawarwarinta zasu isa Najeriya a kwanaki masu zuwa, domin taimakawa da harkokin sadarwa, shirye-shirye da tattaro bayanai. Britaniya tayi alkawarin samar da hotunan tauraron dan-adam, inda kuma Faransa tace zata samar da jami’an tsaro. China da Kanada sune kasashe na baya-bayannan da suka yi tayin taimakawa Alhamis dinnan.
Litinin dinnan ma wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Gamburu dake kusa da iyakar Kamaru da inda suka kashe mutane sama da 200.
Wannan lamarin na Gamburu ya nuna irin gazawar jami’an tsaron Najeriya wajen kiyaye rayukan fararen hula a yankin da ke kara ganin tashe-tashen hankula.