Wannan na zuwa ne mako guda bayan cimma yarjejeniya da kanfanin ya yi tsakaninsa da mahukunta Nijar
Duk da kasancewar kanfanin na kasar China a matsayin mai alfanu ga yankin arewacin Nijar al’umma da mahukuntan yankin sun ce ba su ga wani abin a zo a gani da kanpanin yayi lokacin da yayi aikin hako karfen uranium a Azelik da ke yankin Ingall a arewacin Nijar.
Masu fafutuka da kare hakkokin bil’adama irinsu almustafa Alhassan sun bayyana cewa tsawon lokacin da kanfanin ya shafe yana aiki a yankin sun yi ma yankin illa matuka ga kuma gurbata muhalli.
A shekara ta 2014 ne kanfanin na China ya rufe kofofinsa a cikin wani yanayi na sa-in-sa tsakaninsa da ma’aikatansa to sai dai gamayyar kungiyoyin matasa na jihar Agadas sun fitar da sanarwa ta neman kanpanin ya sake salon yadda yake ayyukan hako karfen uranim a yankin.
Kanfanin na kasar China zai gina katafariyar tashar samar da wutar lantarkin mai aiki da hasken rana a yankin, wadda tana daga cikin abubuwan more rayuwa da al’ummar yankin za su anfana da ita.
Saurari rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna