To saidai wannan na zuwa ne adaidai lokacin da kamfanin Rastom na kasar Rasha mai samar da makamashin nukuliya ke tattaunawa da gwamnatin mulkin sojin Nijar domin karbe aikin hakar uranuim din daga hannun kamfanin Orano na kasar Faransa domin mallaka masa.
A cikin yanayin samar wa kasar Nijar 'yancinta bisa ga sabuwar tafiyar da kasar ke yi ya sa mahukuntan Nijar suka dauki wannan matakin ta hanyar Ministan Kula da Ma’adinai a kasar, inda suka bai wa kamfanin na Orano mallakar kasar Faransa wa’adin ya fara aiki ko kuma a soke lasisisnsa.
Abdurahamane Amma na kungiyar dake sa ido kan makamashi a Agadas ya yaba da wannan matakin da mahukuntan Nijar suka dauka.
A cikin wannan yanayi ne da dama daga cikin 'yan Nijar ke alakanta matakin da sabuwar alakar da ke tsakanin kasar Nijar da Rasha da kuma Iran, ko da yake ga Abdulkareem Anicet na wata kungiya dake fafutukar ganin an raba gari da turawan yamma, idan kamfanin Orano bai soma aiki kafin wa’adin ba a kwace lasisin a bai wa wani kamfanin.
To amma ga Emoud Issouf na kungiyar M62 soma aikin wata sabuwar dabara ce ta kamfanin na Orano wanda ba zai hana kasar Nijar raba gari da Faransa ba.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna