Masu hakar zinari a yankin Jado dake jihar Agadaz, a Jamhuriyar Nijar, sun fara barin wajen, biyo bayan wa'adin da gwamnatin ta ba su.
Sai dai mahakan sun koka da rashin aikin yi idan har aka kore su daga wannan wuri, suna masu cewa ba su da wata hanyar ciyar da iyalansu, lura da cewa ba lokacin damuna ba ne.
Tuni dai wata tawaga da ta hada da Ministan ma’adainai Musa Baraje da shugaban hukumar wanzar da kwanciyar hankali Kanal, Abu Tarka, ta isa Jado, inda ta yi wa jama’a bayani kan yadda ‘yan kasashen waje suka fi amfana saboda sun mallaki kayan aiki, laamrin da mahakan suka amince da shi.
Saurari rahoton wakiliyar Muryar Amurka, Tamar Abari domin jin karin bayani:
Facebook Forum