Ma'aikatar ayyukan jinkai karkashin jagorancin Sadiya Umar Faruk, tare da hadin gwiwar babban bankin duniya ne za ta jagoranci wannan shirin ba da tallafin wanda aka yiwa take da “Rijistar ba da tallafin gaggawa na annobar korona birus.”
Gwamnati za ta raba wannan tallafin da da tsarin bin shiya-shiya a lokaci daban-daban a kasar.
Za’a fara aiwatar da wannan shiri da za’a yi kashi-kashi ne daga gobe litinin a jihohi biyu na shiyoyi biyu inda za’a yi rajista, kuma za’a fara ne da jihohin Bauchi da Adamawa daga shiyyar Arewa maso Gabas daga 24 zuwa 31 ga watan Mayu.
Majiyoyi daga jihar Bauchi sun yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta riga ta tattara bayanan al’umman garurruwa 828 na kananan hukukomi 12 da zasu ci gajiyar shirin tallafin.
Karin bayani akan: SOCU, korona, Coronavirus, Bauchi, Sadiya Umar Faruk, Nigeria, da Najeriya.
Wata sanarwa da da jami'in yada labarai na sashin kula da ayukan jihar wato SOCU a ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar Bauchi, Malam Yakubu Mudi ya fitar, ta tabbatar da wannan labarin.
Malam Yakubu Mudi, ya ce manufar wannan tallafin shi ne ba da agajin gaggawa ga ‘yan kasa ta hanyar zakulowa tare da tallafawa mutane da iyalai a yankunan karkara da birane wadanda annobar korona birus ta yi tasiri ga hanyoyin samun kudadden shigar su.
A jihar Bauchi kawai, an zakulo garurruwa 828 a kananan kukumomi 12 wadanda za su ci gajiyar shirin, baya ga cika sharudan zabar su ta hanyar mayar da martani ga sakonnin wayar tarhon su da lambobi na musamman wanda sashin kula da aiyukan jihar wato SOCU a ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki za ta raba musu a dukannin kananan hukumomin kamar yadda mallam Mudi ya bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa, lamba ta musamman da ake shiga tsarin na kasa ita ce *969# wanda za’a iya latsawa kan wayoyin hannu domin hada mutum da cibiyar ba da tallafin gaggawa na shirin domin neman karin bayani kan tallafin.
Ma’aikatan wucin gadi da aka tura yankunan da za a fara shirin sun fara shiga lunguna da sako domin wayar da kan al’ummar kananan hukumomin da za su ci gajiyar shirin, don su kasance cikin shirin ko-ta-kwana wajen ganin irin sakwannin kan wayoyin su na salula.
An fara yin sanarwa ta hanyar sakwannin radiyo da shirye-shirye na musamman domin wayar da kan al’umma da za su ci gajiyar shirin.
Mallam Mudi ya yi kira ga al’ummar jihar Bauchi da su yi amfani da wannan damar wajen yin rajistar shiga shirin ba da tallafin, tare da neman hadin gwiwar masu ilimi su taimaka a aikin fadakar da al’umma don kada su dauka tsarin na damfara ne.