Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Wanda Cutar Coronavirus Ta Kashe A Najeriya Cikin Kwana Bakwai- NCDC


Gadajen asibiti a Abuja
Gadajen asibiti a Abuja

Hukumar yaki da cututtuka masu saurin yaduwa a Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa ana samun raguwar adadin masu kamuwa da cutar coronavirus a kasar tana mai cewa, a tsawon mako guda cutar ba ta yi kisa ba.

Alkalumman da hukumar ɗakile cututtuka NCDC ta fitar sun yi nuni da cewa a cikin kwana bakwai a jere annobar korona ba ta yi kisa ba a Najeriya, lamarin da hukumar ta ce abin farin ciki ne.

A jimillance, mutum 2,061 ne cutar ta yi sanadiyyar mutuwar su a Najeriya, kuma tun ranar Lahadin makon jiya ya zuwa jiya Asabar ba a samu wanda ya mutu ba sakamakon cutar ta korona.

Sabbin alkalumman hukumar dakile cututtuka masu saurin yaduwa ta NCDC sun yi nuni da cewa mutum 60 ne suka kamu da cutar korona a ranar Asabar, inda jihar Legas ne cutar ta fi kamari da adadi na 22 da suka fi yawa, jihar Rivers na da adadin mutum 15 da suka kamu da cutar, jihohin Bayelsa 7, Kaduna 5, Ogun 4, Akwa Ibom 3, Osun 2, Kano 1 da kuma Ebonyi 1.

A jimillance, mutum 164, 207 ne hukumar NCDC ta tabbatar sun kamu da cutar tun bayan bullarta a Najeriya a watan Febrairun shekarar 2020 inda aka sallami mutum 154, 325 kuma mutum 2, 061 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar ciki har da marigayi tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, Mal. Abba Kyari.

A ranar 17 ga watan Afrilu Kyari ya cika shekara daya da rasuwa, sai tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi da dai sauransu.

Idan ba a manta ba, a ranar 27 ga watan Fabrairu shekarar 2020 ne ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta tabbatar da bullar cutar coronavirus a Najeriya da aka gano a jikin wani dan asalin kasar Italiya da ya shigo kasar a ranar 25 ga watan Februairu daga birnin Milan.

XS
SM
MD
LG