Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Ka’idojin Kare Yaduwar Coronavirus Da Aka Saka A Najeriya


Lokacin da aka yi wa shugaba Buhari, allurar rigakafin cutar COVID-19
Lokacin da aka yi wa shugaba Buhari, allurar rigakafin cutar COVID-19

Da misalin karfe 12 daren ranar Litinin, sabbin matakan da hukumomin Najeriya suka saka don kare yaduwar cutar COVID-19 suka fara aiki.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar ne ya bayyana sabbin matakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya.

Muktar Mohammed, daya daga cikin manyan jami’an gudanarwa a kwamitin ya ce:

  • Tarukan Bukukuwa kamar na aure, kada su wuce mutum 50, kuma an fi so a yi a budadden wuri.
  • Ya zama dole mahalarta tarukan su saka takunkumin rufe baki da hanci.
  • Wajibi ne a rika tsabtace hannaye.
  • Wajibi ne kuma bada tazara.

Fannin Sufuri

  • Ba a kayyade tafiye-tafiye a tsakanin jihohi ba.
  • Amma ana so masu harkar sufuri su bi ka’idojin da ma’aikatar sufuri ta gindaya, a kuma tabbatar an yi amfani da matakan kariya – a kuma tabbatar da an ba da tazara a inda ya kamata.

Ma’aikatun Gwamnati

  • Muna ba da kwarin gwiwar da a ci gaba da aiki daga gida musamman daga ma’aikatan da suke kasa da mataki na 12
  • Wadanda suke mukamin aiki na 12, za su iya komawa ofis.

XS
SM
MD
LG