Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Dakatar Da Shirin Karin Kudin Wutar Lantarki


Majalisar Wakilan Najeriya
Majalisar Wakilan Najeriya

Majalisar Wakilan ta bayyana lamarin a matsayin “rashin imani da rashin tausayi” ga ‘yan Najeriya, a daidai lokacin da komadar tattalin arzikin kasa da annobar korona da kuma karin farashin man fetur suka haifar da tashin farashin kayan masarufi da sufuri da yawaitar rashin aikin yi.

Biyo bayan korafe-korafen ‘yan Najeriya, Majalisar wakilai ta bukaci hukumar kula da kayyade wutar lantarki ta kasa (NERC) da ta dakatar da shirin ta na kara kudin wutar lantarki a watan Yuni mai zuwa.

Dan majalisar wakilai Aniekan Umanah ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, sakamakon abin da ya kira “kara uzzura matsin tattalin arziki ga ‘yan kasa sakamakon kara tsadar rayuwa.”

Umanah ya bayyana matukar damuwa da yadda aka sabawa tanadin dokar sashen makamashi ta shekarar 2005, wadda ta kafa hukumar ta NERC, ta kuma dora mata alhakin ba da lasisi ga kamfanonin samarwa da rarraba wutar lantarki.

Haka kuma ya ce hukumar na da hakkin kula da tabbatar da tsari da ingancin ayukan kamfanonin, ta yadda za su cimma bukatun jama’ar da ke hulda da su, kazalika da kuma kayyade farashin lantarkin daidai da yadda ake biyan bukatun na jama’a.

To sai dai kuma akasin haka ne ke faruwa in ji dan majalisar, ta yadda “rashin samar da wutar lantarkin ya yi mummunan tasiri a haujin ci gaban kasa ta bangaren tattalin arziki.”

Rahoton hukumar ba da lamuni ta duniya IMF na shekarar 2020, ya bayyana cewa kamfanonin sarrafa kayayyaki a Najeriya sun yi asarar kudi dalar Amurka biliyan 200 sakamakon rashin wutar lantarki, yayin da kuma ‘yan Najeriya suka kashe zunzurutun kudi har dala biliyan 21 akan injunan samar da wutar lantarki.

A yayin da take amincewa da kudurin a zaman ta na ranar Alhamis, majalisar wakilan tace tana sane da cewa hukumar ta NERC da kamfanonin rarraba wutar lantarki, DISCOS, sun yi karin farashin wutar lantarki har sau 5 daga shekarar 2015 kawo yanzu. Na baya-bayan nan shi ne karin da aka yi a watan Janairun wannan shekara ta 2021.

Majalisar Wakilan Najeriya
Majalisar Wakilan Najeriya

To sai dai ta ce duk da wadannan kare-karen farashin, har yanzu ‘yan Najeriya na fama da matsalar rashin isasshiyar wutar lantarki a kullum, ga kuma cajin makudan kudaden iska da ake yi wa kashi 50 cikin dari na abokan huldarsu, bisa kiyasi na rashin mita.

Majalisar wakilan ta kuma amince da cewar rashin samun isasshiyar wutar lantarki kamar yadda ya kamata, ya taimaka sosai wajen gurgucewar tattalin arzikin ‘yan kasa.

Haka kuma majalisar ta lura da mummunan yanayin da ‘yan Najeriya suke ciki a halin yanzu na tabarbarewar sha’anin tsaro sakamakon yawaitar ayukan ta’addanci, hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane domin karbar kudin fansa, da rikicin manoma da makiyaya wanda ya gurgunta sha’anin noma abinci, da dai sauran ayukan assha daban-daban da suke salwantarda rayuka da dukiyoyi, kazalika da raba dimbin al’umma da gidajensu.

Majalisar wakilan ta bayyana damuwar cewa a daidai lokacin da gwamnatoci a duk fadin duniya suke kokarin sassautawa jama’arsu, tare kuma da ba su tallafin rage radadin bala’in da annobar Korona ta jefa su, sai ga shi hukumar ta kula da kayyade farashin wutar lantarki ta Najeriya tana kokarin kara matsantawa ‘yan kasa, ta hanyar kara kudin wutar lantarki, bayan karin da ta yi a farkon wannan shekara.

Ta bayyana lamarin a matsayin “rashin imani da rashin tausayi” ga ‘yan Najeriya, a daidai lokacin da komadar tattalin arzikin kasa da karin farashin man fetur suka haifar da tashin farashin kayan abinci da na masarufi da kuma sufuri, a yayin da kuma rashin aikin yi ke dada karuwa.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Instagram/speakergbaja)
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Instagram/speakergbaja)

Akan haka majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta umarci hukumar ta NERC, da ta soke matakin nata na karin kudin wutar lantarki da ta shirya somawa a watan Yunin shekarar nan ta 2021, bisa la’akari da mawuyacin halin da ‘yan kasa suke ciki.

Haka kuma ta umarci kwamitocin ta akan makamashi da na yaki da fatara, da na kwadago da su tabbatar da an bi umarnin majalisar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG