Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Sabon Hari A Wani Kauyen Maiduguri


A yammacin ranar Talata, wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari kan unguwar Jiddari Polo dake garin Maiduguri inda suka dinga harba manya-mayan bindigogi da kuma wasu ababe masu fashewa.

Wannan harin na jiya da maraice dai, ya zo ne a dai-dai lokacin da al’umma ke shirrin shan ruwan buda baki. Ganin cewa mutanen da dama a wannan yankin suna azumi.

Ko da shike irin wannan harin ba shine na farko ba da wadannan mahara kan kai wa al’umma wanda kusan shekaru uku a jere suke ta kai wa cikin azumin watan ramadan. Abun da ke sa mutanen angwanin ke ficewa daga angwaninsu.

Da yammacin jiya ma, sai da mutane daga Jiddare Polo suka dinga ficewa daga angwansu.

Karin bayani akan: Maiduguri​, Adamu Dan Borno, Jiddare Polo, Muryar Amurka, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.

Muryar Amurka ta zanta da wadansu mazaunan irin wadanan anguwanin ta wayar tarho inda suka shaida cewa, maharan da kafa suka shigo musu, suka yi ta harbe-harbe amma sun samu sun gudu.

Malam Adamu Dan Borno, wani mazaunin angwan ya ce har yanzu basu ga wani aikin gwamnati ba game da yaki da Boko Haram domin ya ci a ce, akwai shirin da kafafen yada labarai suke yi don mayar musu da martini a ilmance domin duk abin da suke yi, su na yi da sunnan addini ne ya nuna masu, alhalin karya suke yi wa addini, amma har yanzu gwamnati ta kasa yin wannan.

Yanzu haka dai, babu takamanman bayani game da wannan harin da ake ce mayakan sun kai Jiddare Polo bale a san irin barnan da za’a ce sun aikata.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG