Bayanai suna nuni da cewa hare-haren da 'yan bindiga suke ta kai wa jami'an tsaro a kudu maso gabashin Najeriya yanzu ya zamo wani batu na gama-gari, da kuma wani al'amarin da ke ci gaba da haddasa wani yanayi na fargaba a zukatan al'umar wannan yankin.
Wasu dai na cewa dole ne a fuskanci yanayin fargaba a yankin kudu maso gabas saboda yadda tsaro ya tabarbare a tsawon watanni kalilan, wato daga watan Satumban bara zuwa yau.
Misali, a jihar Abia, wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a gano ko su waye ba sun kai farmaki wasu 'yan sanda biyar a karamar hukumar Ohafia, inda suka kashe dan sanda guda da kuma jikkata sauran hudun a watan Satumban shekara ta 2020.
A watan Fabrairun da ya shude kuma, wasu 'yan bindiga sun harbe wani dan sanda har lahira a ofishin 'yan sanda da ke garin Omoba na karamar hukumar Isiala Ngwa South; kana a watan Fabrairun kuma, wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu a ofishin 'yan sanda da ke unguwar Abayi a garin Aba.
A watan Maris da ya wuce, wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani shingen 'yan sanda a garin Abiriba da ke karamar hukumar Ohafia, inda suka kashe 'yan sanda ukku.
Hakazalika a jihar Ebonyi, wasu 'yan bindiga sun kai farmaki wani ofishin 'yan sanda da ke garin Onueke na karamar hukumar Ezza South, inda suka kashe 'yan sanda uku a watan Janairun wannan shekarar.
A watan Febrairun da ya gabata kuma, wasu 'yan bindiga sun cinna wa shelkwatar 'yan sanda da ke garin Isu na qaramar hukumar Onicha wuta; sa'annan a watan Maris din nan da ya wuce, wasu 'yan bindiga sun kona shelkwatar 'yan sanda da ke garin Iboko na qaramar hukumar Izzi.
A jihar Anambra kuma, wasu mahara a watan Maris da ya gabata sun kashe 'yan sanda hudu da sojojin ruwa uku kusa da hanyar garin Neni da ke karamar hukumar Anaocha, tare da kona motar zirga-zirgarsu da kuma arce da bindigoginsu.
A cikin watan ne wasu maharan kuma suka kashe dogaran gidan yari biyu da kuma afka wa wani ofishin 'yan sanda da ke garin Ekwulobia na karamar hukumar Aguata.
Kana a jihar Imo a watan Fabrairun da ya shude, wasu 'yan bindiga sun qona shelkwatar 'yan sanda da ke karamar hukumar Aboh Mbaise, kuma suka kashe 'yan sanda biyu a shelkwatar 'yan sanda da ke garin Umulowo a karamar hukumar Obowo.
A watan Maris kuma, wasu maharan sun kona ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Ihitte/Uboma.
Sannan wasu 'yan bindiga sun kai hari a gidan gyara hali na Owerri suka saki fiye da fursunoni 1,800, tare da cinna wa motoci da yawa a shelkwatar rundunar 'yan sandan jihar wuta.
An kuma kai hari a wani sansanin soji da ke unguwar Ukwuorji a Owerri aka kona motoci biyar, har da ma soja guda a ciki; an far wa shelkwatar 'yan sanda a karamar hukumar Ehime Mbano an saki wadanda ake zargi da aikata laifuka, tare da kona shelkwatar da motoci; sa'annan an kai hari shelkwatar 'yan sanda a garin Mbieri an saki wadanda ake zargi da aikata laifuka.
Wani abu da kuma ya zo wa mutane a yanayi na ba-zata, shi ne wani hari da wasu ‘yan bindiga suka a gidan gwamnan jihar ta Imo Hope Uzodinma a karshen watan Afrilu inda suka kashe jami’in tsaro biyu.
Yanzu da ya ke alhaki ya rataya ne akan gwamnonin shiyyar kudu maso gabas su kare al'umomin jihohin nasu, jama'a na ganin cewa gwamnonin su ma sun kasa warware wadannan matsalolin saboda har yanzu lalube suke yi a duhu a yunkurin gano ainihin musabbabin hare-haren da kuma su waye ke aikata su.
Wasu dama sun yi ta zargin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, amma kungiyar ta nesanta kanta da wadannan hare-hare.
Yanzu a yayin da wannan ayar tambayar gano dalilan da ya sa 'yan bindiga suke far wa jami'an tsaro a shiyyar kudu maso gabas ke yawo a sarari, ra'ayoyi mabanbanta sun bayyana game da batun.
A wata hirarsa da jaridar Vanguard, Mazi Okechukwu Isiguzoro, tsohon shugaban kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo, ya ce 'yan bindiga suna far wa jami'an tsaro ne domin su cusa wa gwamnati da jama'a tsoro da zummar cimma muradun kansu.
'Wadannan hare-haren ba za su rasa nasaba da fushin da ake yi wa wasu bata-gari da ke cikin rundunar 'yan sanda ba, wadanda suke ci wa al'umma tuwo a kwarya,' inji wani mazaunin garin Aba, Kwamred Goodluck Egwu Ibe, yayin da ya ke hira da jaridar Vanguard.
Kazalika, wani wanda bai so a ambaci sunansa ba ya ce mai yiwuwa takaici da fushin da ake yi wa gwamnati mai ci ne suka janyo hare-haren.
Ya kara da cewa tana yiwuwa kuma mutanen da suke fushi da rashin kwarewar gwamnati, da tsare-tsarenta mara dadi, da kuma rashin tausaya wa talakawa ne yasa wasu suka yanke shawarar zazzage fushinsu akan jami'an tsaro.
Ya kara da cewa, watakila rashin aiki na daya daga musabbaban hare-haren, da yake akasarin matasa ba su da sana'a, kuma ana iya yin amfani da su wajen haddasa fitintinu.
Dakta Celestine Nwosu kuma ya shaida wa Muryar Amurka cewa watakila gazawar gwamnatin tarayya wajen daidaita bukatun masu zanga-zangar #EndSARS ce musabbabin far wa jami'an tsaron da 'yan bindiga ke yi.
Ya kara da cewa kin ganawa da rukunoni daban-daban da ke fafatuka mabanbanta, kamar cin gashin kai da kuma sabunta fasali na daga cikin masabbaban kai wa jami'an tsaro hari, a matsayin hanyar bayyana fushi da rashin amincewa.
Kana ya ce tana yiwuwa 'yan bindigan suna fushi ne da sassauta wa 'yan ta'adda da kuma fatattakar masu zanga-zangar lumana da gwamnatin tarayya ke yi.
'Mahara da masu garkuwa da mutane duk abin da suke so a kowane lokaci su ga sun karya lagon wani sashe na gwamnati. Ita rundunar 'yan sanda wani sashe ne na gwamnati. Toh yayin da aka rage mata karfi sai kuma a samu dama a rika far wa jama'a ba tare da wata wahala ba, miyagu su rika cin karensu babu babbaka,' in ji Malam Suleiman Balarabe, wani lauya kuma kwamishinan 'yan sanda mai ritaya.