Ana zargin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Sanata Ali Modu Shariff da shirya kai harin.
Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Borno shi ya fitar da sanarwar wadda ya aika wa manema labarai ta hanyar yanar gizo. Yace suna cikin tawagar da misalin karfe hudu da rabi ranar Lahadi sai wasu da ake zaton magoya bayan Ali Modu Sheriff ne suka far masu akan titin Sir Kashim Ibrahim. A lokacin suna zagayawa asibitoci daban daban domin tallafawa marasa galifu. An far masu ne a daidai inda ofishin kemfen din Ali Modu Sheriff yake. An farfasa gilashin motocinsu kusan guda goma.
Shugaban APC din yace bisa duka alamu tsohon gwamnan ne yasa aka kai masu harin. To saidai an kira magoya bayan jam'iyyar APC kada su kuskura su mayarda martani. Shugaban APC yace amma zasu bi kadun lamarin yadda ya kamata.
Amma shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Borno Alhaji Baba Basharu wanda yace ofishin UTC wurin da lamarin ya faru ba na PDP ba ne amma na Ali Modu Sheriff ne. Sabili da haka ba za'a ce 'ya'yan jam'iyyar PDP suka aikata aika aikar ba. Shi ma mai magana da yawun Ali Modu Sheriff Inuwa Bala yace baya gari saboda haka ba zai iya cewa magoya bayansu suka aikata ko kuma basu ba ne.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu