Talatannan ne bama-bamai uku suka tarwatse a wasu wurare a arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan lamarin ya kara tayar da hankalin mutane musamman sabili da alwashin da kungiyar Boko Haram tayi cewa zata wargaza shirin zaben da yake karatowa.
A cikin rahoton farko da wakilinmu ya aiko yace bamabaman farko sun tashi ne a wurin da sojoji suke binciken ababen hawa da mutane a garin Biu dake jihar Borno. Nan take mutane 12 suka mutu.
Masu yada labarai na yankin sun ce ‘yan kunar bakin waken suna cikin keken napep yayinda sojoji suka tsayar domin su bincikesu.
Da saukarsu daga keken din sai suka tayar da bam.
Wasu rahotanni kuma sun ce sojoji sun mayarda martini har suka kashe ‘yan ta’adan 17.
Hari na biyu ya faru ne a garin Potiskum dake jihar Yobe. Yansanda sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tarwtsa kansa inda ake sayar da abinci ya kashe mutane uku, 12 kuma suka jikata.
Yan Boko Haram sun sha kai hare-hare a garuruwan Biu da Potiskum.
A wata sabuwa kuma an ji karar fashewar wasu abubuwa da ake zaton bamabamai ne da kuma karar bindigogi a wurin da jam’iyyar adawa ta APC ke yin gangamin zabe a garin Okrika dake kudancin jihar Rivers.
Jam’iyyar APC tana kalubalantar PDP mai mulki a zabukan da za’a gudanar watan gobe.
Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin fashewar bamabaman.
Ga rahoto kan fashewar data auku a Potiskum.