Shugabannin sun yi gargadin ne a taron zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista wanda aka gudanar a harabar mijami'ar ECWA dake Bauchi.
Malam Usman Shagari Adamu wanda ya jagoranci al'ummar musulmi a taron yace babban makasudin taron shi ne samarda zaman lafiya. Yace sun fara samo bakin zaren kuma sun fara dinke barakar dake akwai tsakanin mabiya addinan biyu. Yace sun taru a cilkin coci domin su hada kansu su warware matsalolin da suke fuskanta. Yace mafita ita ce su ajiye banbancin siyasa ko na addini ko na kabila su dawo saboda zaman lafiya.
Rev Dr Shuaibu Gyel wanda aka gudanar da taron a mijami'arsa yace manufarsu ita ce son zama lafiya. Idan akwai wani da yake yin abun da ya ga dama sai su ja masa hankali da hadin kansu. Kada ya samesu da rabuwar kawuna. Idan dan siyasa yana yin kalamansa sai su nuna masa abun ba daidai ba ne. Idan kuma ana muzgunawa jama'a sabili da addini, ko kabilanci ko siyasa to ba abun da addin ya koyas ba ke nan.Kowa ya san akwai ranar shari'a da kowa za'a tambayeshi abubuwan da yayi.
Alhaji Garba Muhammad Noma jarman Bauchi yayi tsokaci akan irin maganganun da wasu keyi. Yace yin hakan ba zai taimakawa zaman lafiya ba. Wasu suna anfani da kafofin yada labarai na gwamnatin tarayya da makamantansu suna fadan abubuwan da zasu cutar da kasar gaba daya. Musamman ana son a hada wa arewa rigima ta wajen addini da kabilanci. Kasar ma gaba daya ana son a haddasa rigimar addini. Ana maganganun bata wani addini ko wani jinsi a kasar. Zaman lafiya ba zai yi kyau ba da irin wadannan kalamomin.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.