Mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu sun bayyana irin azabar da suka sha wa kwamitin tantance ta'adi da gwamnatin tarayya ta kafa ya kai ziyara domin sanin halin da suke ciki.
Kwamitin ya ziyarci sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu da kuma duk kananan hukumomin da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram domin tabbatar da halin da ake ciki.
'Yan kwamitin a karkashin tawagar da Alhaji Musa Zakari ke jagoranta sun yi jawabi bayan sun fito daga fadar sarkin Mubi. Shugabansu yace babu wanda zai cewa mutanen garin su dawo da ya wuce sarkin garin. Shi sarkin garin ya dawo da kansa saboda haka duk wani mazaunin garin Mubi ya dawo saidai idan zaman Mubin bai dameshi ba.
Kwamandan rundunar sojojin dake Yola yace kawo yanzu sun kwato duk kananan hukumomin dake hannun 'yan Boko Haram in ban da Madagali. Ko nan ma suna cigaba da fafatawa har sai sun kwato yankin wannan makon. Yace suna aiki da 'yan kato da gora wadanda suke basu labarun asiri.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz