Akan haka ne Wakilinmu Umar Faruk Musa, yayi hira da wani mai fashin baki akan alamura a Najeriya, Malam Shuaibu Mungadi,Yace “ ba mamaki idan ya nuna sha’awa kuma ba mamaki idan yayi burus,amma idan yayi burus aikin masu bashi shawara ne su lurar dashi, kada ga manta daga cikin masu bashi shawara ada akwai wani da ake kira Ahmed Gulak, wanda shi ke bashi shawar akan harkokin siyasa kuma shi da yankin da yanzu ake fama da fitinu-fitinu ne yakamata iri-irinsu, sun nuna masa cewa yakamata shugaban kasa ka tafi wuri kaza, kar ka manta, a ranar da aka yi kisan wasu dalibai a wannan yanki da kuma boma-bomai a Nyanya, yana Kano, yana raye-raye,wannan yakara nuna ko oho dashi da masu bashi shawara ke yi.”
Ya kara da cewa “ bai dace ba a koina a duniya ace an sarrafa rayukan yaran mutane wadanda bazu jiba basu gani ba akan rikicin da akeyi a kasa an sarrafa rayukansu da na iyayensu, an jefa su cikin tsaka mai wuya kuma shugaban kasan nan yana zaune, bayan ko shuwagabanin duniya karka manta fa ana cikin wannan hada-hadan sace wadan nan yara ne fa,a wannan lokaci ne shugaban kasa ya kira wani taro a tattalin arziki na duniya,yakamata idan masu bashi shawara suna bashi shawaran gaskiya da sun bashi shawaran a dage wannan taron,kuma taron da akayi farkon tattaunawan da aka yi akan maganar yaran ne.”
Yanzu babu shakka abubuwan dake gaban ‘yan Najeriya,suna da daman na farko,yanda ‘yan kasashen wajen nan dake shigowa zasu kubutar da yaran da kuma cewa gwamnati ta duba tayin da ‘yan boko haram suka yi cewa zasuiya sako wannan yaran.