Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Gwamnati ta Gaggauta Yin Sulhu da Boko Haram


Obiageli Ezekwesili, tsohowar Ministar Ilimi na jawabi akan 'yan matan da aka sace, a Abuja, Najeriya.
Obiageli Ezekwesili, tsohowar Ministar Ilimi na jawabi akan 'yan matan da aka sace, a Abuja, Najeriya.

Mahaifin daya daga cikin yaran da aka sace yace,yana farin ciki ganin hoton bidiyon da ‘yan boko haram suka fito dashi,domin ya ga wata mai kamar ‘yar sa a ciki.

Daya daga cikin iyayen yaran da aka sace a Chibok Malam Shattima yace,yana farin ciki ganin hoton bidiyon da ‘yan boko haram suka fito dashi,domin ya ga wata mai kamar ‘yar sa a ciki.

Yace yana rokon gwamnati dasu gaggauta neni ‘yan Boko Haram ayi sulhu domin dawo da yara da suka sace da kuma kawo karshen hare-hare a Najeriya baki daya.

Ya kara da cewa alhakin nemo yaran nan ya rataya ne akan gwamnati ganin cewa a hannun su aka sace su,domin su bi umanin gwamnati na cewa su kai yara makaranta,
wanda yace yana mai nuni da cewa yaran nan na gwamnati ne.

Malam Shettima, yace yakamata gwamnati,tayi duk abunda ya dace domin ganin an samu karbo yara nan domin iyaye su samu sa’ida.

Idan dai ba 'a mantaba sama da yara 'yan makaranta mata dari biyu ne aka sace a makaranta a garin Chibok kimanin wata daya kennan.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG