Kamfanin mai na Shell yace ya toshe man da yake tsiyaya a cikin ruwan teku kusa da gabar Najeriya, kuma ya katse kusan dukkan man da ya taru a kan ruwan kafin ya kai ga gabar wannan kasa dake Afirka ta yamma.
A cikin sanarwar da ya bayar litinin, kamfanin na Shell yace zai ci gaba da sanya idanu a inda man ya tsiyaye, zai kuma kwashe duk wani man da ka iya sake taruwa. Kamfanin an Shell yace wani man da yake tsiyaya daga wani kamfani dabam ya kawo cikas ga kokarinsa na kawar da mansa da ya tsiyaye, amma kuma yana kokarin kawar da wannan mai da ya tsiyaye na daya kamfanin.
Reshen kamfanin man Shell na Najeriya yayi kiyasin cewa yawan man da ya kwarara cikin ruwan tekun bai kai ganga dubu 40 ba. Wurin hakar mai cikin teku da ake kira Bonga, inda wannan tsiyaya ta faru, na iya samar da ganga dubu 200 na danyen mai a kowace rana. Kamfanin ya dakatar da hakar mai a rijiyoyinsa dake wannan wuri har sai illa ma sha Allahu.
Kamfanin yace an gano man ya tsiyaye ne daga wani bututun da yake jigilar mai daga dandalin haka zuwa cikin tankokin da ake ajiye shi kafin a yi lodinsa.