A dai dai lokacin da kungiyar kwadago a Najeriya ke shirin shirya gangamin yajin aiki domin nuna rashin amincewa da janye gatancin da Gwamnati ke yiwa farashin man fetur, sai gashi manyan jami’an gwamnatin Najeriya sun dukufa-ka’in da na’in wajen kokarin wayar da kan ‘yan kasar game da alfanun dake tattare da cire gatancin.
A rahoton da wakilin Muryar Amurka a birnin tarayyar Nigeria, Abuja, Nasiru Adamu el-Hikaya, ya aiko anji Gwamnan babban bankin Nigeria Sunusi lamido Sunusi yana bayanin irin alfanun da ‘yan Najeriya zasu samu idan an cire gatancin.
Sanusi Lamido Sanusi, shi ya fara magana kafin jami'an kungiyar kwadago ta Najeriya a cikin wannan rahoto.
Saurari Rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya |