Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidan Rediyon Biyafara Yana Aiki Har Yanzu Duk Da Cewa


Na'urorin yada shirye shiyen gidajen Rediyo.
Na'urorin yada shirye shiyen gidajen Rediyo.

Kamar yadda aka saurara a safiyar Asabar 18 ga watan Yuli, tashar tana nan tana yada shirye shiryenta.

Masu farfaganda a tashar gidan rediyon Biyafa, sun musanta ikirarin da Gwamnatin tarayya ta Najeriya tayi cikin makon nan cewa ta dakile tashar tareda kama ma'aikata da kama kayan aikinsu.

A cikin rahoton da wakilin Sashen Hausa, Babangida Jibril, ya aiko mana, an ji wani mai gabatar da shirye shirye yana cewa "Mutane suna sauraron wannan huduba....sun ce bamu da kudi, duk da haka mune na daya a jerin gidajen rediyo a duk fadin duniya.

Ya ci gaba da cewa, "sun ce mu ba 'yan Jarida bane, kan wannan na yarda", mai gabatar da shirye shiryen ya ci gaba da cewa, "amma muna da wani abu da baku dashi, shine gaskiya". Daga nan sai ya juya harshe ya fara magana da harshen Igbo.

Idan za'a iya tunawa a farkon wannan makon ne lokacinda manyan ma'aikatan ma'aikatar yada labarai suka kaiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara, a bayan ganawar, babbar Darektar ma'aikatar, ta gayawa manema labarai cewa, an dakile tashar rediyon, saboda yana gabatar da shirye shiryensa ba tareda lasisi ko izinin gwmnati ba.

Kwana biyu bayan wannan sanarwar, sai kuma Darektan hukumar kula da kafofin sadarwa musamman gidajen rediyo da talabijin,watau NBC, Mr. Imeka Mbah, ya fito ya gayawa duniya cewa, jami'an tsaro sun kama ma'aikatan gidan rediyon, sun kuma kwace kayayyakin aikinsu.

Wani da aka saurara a tashar rediyon ranar Asabar, yace wadannan jami'an suna yaudarar shugaban kasa ne kawai, babu wani ma'aikacin gidan rediyon da aka kama, ko aka kwace musu kayan aiki.

Mai maganar yace tashar tana yada shirye shiryenta domin fadakar da al'umar Igbo kan irin cin-zalin da ake yiwa 'yan kabilar a Najeriya. Tareda da kuma zummar sake farfado da burin kafa kasar Biyafara.

Wani mai sharhi a Jami'ar Bayero ta kano, Dr. Abubakar Alhassan, ya gayawa Babangida Jibril cewa, Gwamnati tana iya magance wannan lamari ta wajen amfani da dokoki da suke cikin aikace aikacen hukumar NBC.

Shima da yake magana da Mahmud Lalo, darektan hulda da jama'a na hukumar NBC Mallam Awwal Salihu yace, a iya saninsa gidan rediyon baya aiki, idan kuma suna aiki, gwamnati tana daukar matakai na hana haka.

Ga karin bayani.

Gidan Rediyon Biyafara Yana Aiki Har Yanzu Duk Da Cewa - 3'18"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG