Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilas Yaro Da Ya Kai Shekarun Karatu Ya Shiga Makaranta--Gwamna Ganduje


Gwamna Rochas Okorocha, da Gwamna Rabiu Kwankwaso tare da Sarki Sanusi a fadar gwamnatin Jihar Kano.
Gwamna Rochas Okorocha, da Gwamna Rabiu Kwankwaso tare da Sarki Sanusi a fadar gwamnatin Jihar Kano.

Daga yanzu duk yaro da ya kai shekarun karatu tilas a sakashi makaranta, inji Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar kano.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka lahadin nan da yake maida jawabin gaisuwar Sallah da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kai masa a fadar gwamnatin jihar, a zaman wani bangare na hawan Nasarawa, da sarki yake yi bayan Sallah, inda suke musayar jawabai da Gwamna.

Gwamna Ganduje yace gwamnati zata yi amfani da masu unguwanni da dagatai wajen tabbatar da yara da suka kai shiga makaranta sunyi haka. Ya kara da cewa malamai na addini masu yawo da almajirai, suma tilas yaran da suke yawo dasu su shiga makaranta, su kuma malaman, a dauke su a zaman malaman addini.

Malaman addinin da basu amince da haka ba, to tilas ya bar jihar Kano, domin ba zai amince kano ta zama matattarar almajirai ba.

Gwamna Ganduje, ya gayawa Sarki Sanusi cewa, gwamnatinsa zata yi kwaskwarima ga shirin bada gurabun karo ilmi a kasashen waje, ta yadda daliban zasu kasance masu koyo sana'o'i su kasance masu dogaro da kansu.

Tunda farko a nasa jawabin, Sarki Muhammadu Sanusi II, yace akwai bukatar masu iko su tuna saduwa da Allah, wanda zai tambayesu yadda suka kare mutuncin talakawa, da lafiyarsu, da dukiyarsu.

Sarki Sanusi, ya bada shawarar a lura da bukatun jama'a, kama daga kiwon lafiya, da ilmi da sauransu.

A lokacin hawan Nasarawar ce sarkin kano, yake amsa gaisuwar talakawa.

Ga karin bayani.

Tilas Yaro Da Ya Kai Shekarun Karatu Ya Shiga Makaranta--Gwamna Ganduje - 3'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG